Wednesday, January 17, 2018

Magidanci Ya Kashe Matarsa Ta Hanyar Lakada Ma Ta Dukan Tsiya A Jihar Jigawa



Rundunar ‘Yan sandan jihar Jigawa sun cafke wani magidanci dan shekaru 50 da ya kashe matarsa ta hanyar lakada mata dukan tsiya a garin Daurawa dake karamar hukumar Birnin kudu a jihar Jigawa
Kakakin ‘Yan sandan jihar, SP Jinjiri Abdul ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce, magidanci ya kashe matarsa da duka ne bayan dan wani sabanin da suka samu a tsakaninsu.
Ya ce, a yanzu haka dai sun yi nasarar kama magidancin tare da tsere shi a wajensu kuma za a garzaya da shi kotu

No comments:

Post a Comment

Pages