KURAKURAI CIKIN FIM DIN ABBA NA
1-A lokacin da iyayen Nabila suka rasu shin dama ita ba ta da wani dangi sai Bukar da Lawan kannen mahaifinta? duk ina dangin mahaifiyarta har aka bayar da ita tsawon wannan lokacin babu wanda ya neme ta?
2- Akwai lokacin da Abban Nabila ya biya kudin sadakinta dubu goma a ka’idar shari’ar musulunci sadakin mace budurwa ya fi yadda suka fada.
3- An nuna ana bukin Umar da Nabila har ana cewa gobe daurin aure amma da aka nuno gidansu Umar da Nabila babu wata alamar ana buki ko mutum daya babu a gidajansu.
4- akwai wurin da Abban Nabila yake bai wa su Umar tarihin yadda ya sami Nabila amma da a ka dawo daga labari sai mai kallo ya ga Umar din baya wajen.
5- A ka’idar musulunci idan mijin mace ya rasu ba ta sake kula wani ko ta yi maganar aure har sai ta yi idda amma sai ga shi lokacin da Umar ya zo yi wa Nabila gaisuwa ana cikin makoki sai ga shi tana yi masa maganar aure.
6-A gidansu Nabila an nuna su kadai ne kuma ba sa kiwon komai kuma gidane mai kyau wanda ba zai kasance a ce idan ma ana kiwo ba zuwa har cikin harabar gidan yadda kowa zai gansu ko kuma a dinga jiyo kukansu amma sai ga shi masu kallo suna jiyo kukan zakaru da karar dakan turmi bayan gidan su kadai ne.
7- Yakamata a ce an nuna mahaifiyar Umar ko sau daya ne ta zo gidansu Nabila ta duba mahaifinta ko kuma a ce an ganta ta zo yi musu gaisuwar mahaifiyarta da ta rasu kasancewar kwana daya ne ya rage a daura auren Umar da Nabila mahaifiyar ta rasu.
8- Ba a nuna lokacin da Abban Nabila ya fada mata cewar shi ba mahaifin ta ba ne daga baya sai mai kallo ya ji tana ba da labarin abin da ya faru tana karama kuma lokacin da aka dauko ta ta yi kan kanta ace ta tuna duk abinda ya faru.
9- Yakamata a ce an nuna karshen Lawan da Bukar saboda sako ga irin masu aikata irin halayyarsu.
No comments:
Post a Comment