
Wani matashi dan shekaru 34, Bisi Adebiosu, a ranar Juma’a ya bayyanawa kotun majistare na Tinubu da cewa tsautsayi ya sa shi gatsar hancin matarsa har sa da ya cire ma ta naman hanci.
Bisi Adebiosu, ya kasance ya zama a gidan mai lamba No. 34 a layin Verimacqueen Str. da ke Lagos Island a jihar Legas, an gurfanar da shi a gaban kotu ne bayan an caje shi da aikata laifuka 2 wadanda suka hada da cin zarafi da yiwa dan Adam rauni.
Lauyar da ya mika karar zuwa kotu, Sifeto Nurudeen Thomas, ya bayyanawa kotun cewa wanda ake zargi ya aikata laifin ne a 9 ga watan Junairu a gidan ma’auratan.
Thomas ya ce a ranar wanda ake zargi ya yiwa uwargidansa wacce ta kasance ma’aikaciyar kiwon lafiya sannan kuma uwar ‘ya’yan sa rauni ta hanyar gatsa ma ta hanci da hakurarsa har sai da ya cire ma ta naman hanci.
Ya ce ma’auratan, sun yi aure a shekarar 2007, inda ya ce sun samu wani dan rikici ne a tsakaninsu a yayin da matar ta samu aiki a wani asibiti mai zaman kansa.
Ya ce mijin matan da aka yiwa rauni, yana da shagon siyar da kaya a gaban gidan da suke zama, a yayinda ya fara gunaguni a kan irin kallar shigar da matan na sa ke yi zuwa wurin aiki.
“Adebiosu ya yiwa matarsa dukan tsiya sannan kuma ba wai yana kula da iyalansa ba ne.” Laifin da ya aikata ya sabawa sashe 11(a) (b) na dokar cin zarafin dan Adam, 2007, da uma sashe 176 na dokar laifuka ta jihar Legas, 2015.
A yayin da sashe 11(a) (b) ta yankewa duk wanda aka kama da irin wannan laifin a garkame shi a gidan yari na tsawon shekaru 5 ko kuma ya niya diyyar naira N100,000 sannan kum sashe 176 ta yanke hukuncin daurin shekaru 3 ga duk wanda aka kama ya aikata irin wannan mummunar aiki.
Shi wanda ake zargi, ya furta aikata laifin da aka laifin yiwa matarsa rauni amma ya karyata laifin cin zarafin ta.
Adebiosu, ya fadawa kotun cewa tsautsayi ya sa shi gatsa hancin matarsa sannan kuma ya duk hakan ni ba a cikin hayyacinsa ba don ya fusata a yayin da ya aikata hakan.
Wanda ake zargi ya fadawa kotun cewa a ranar abun ya faru, ya dawo gida sai ya samu ‘ya’yan su gida suna kuka sannan ya tambaye su ina mahaifiyar na su ta ke, sai suka fada masa cewa ai tafi wani gida da ke layinsu halarta wani casu wato party.
“Da isa na wurin sa na hango ma ta na ta ida shan kwalban giyan Stout na 4 tare da wasu mazan banza; sai da na sa ta dole ta biyo ni gida, a yayin da mu ke sa-in-sa da ita, sai na gatsa hancinta ba tare da sani na ba. “Ina iya kokari na wajen kula da iyalai na, amma mai daki na ba ta girmama ni yadda ya kamata a matsayi na na mijinta.”
Alkalin kotun, Mrs. Kikelomo Ayeye, duk da haka, ta bada umurnin a garkame wanda ake zargi a gidan yarin Ikoyi da ke jihar Legas. Ayeye ta daga saurarar karar zuwa 12 ga watan Fabrairu 2018.
No comments:
Post a Comment