Sunday, January 14, 2018

Bance inason shugaba Buhari ba da aure: Kage akamin - Inji Fati Shu'uma



fina-finan Hausa, Fati Shu'uma ta fito ta karyata wani labarin kanzon kurege da ake yadawa akanta, wai tace tana son shugaban kasa Muhammadu Buhari da aure, jarumar tace tabbas tana son shugaba Buhari a matsayin shugaban al'umma na gari amma ba da maganar aureba kamar yanda ake yadawa.

KARANTA:- Watar Sabuwar Babban Burina Shine In Auri Shugaban Kasa Muhammed Buhari - Jarumar Hausa Film Fati Shu'uma

A wani gajeren bidiyo data wallafa a dandalinta na sada zumunta da muhawara, Fati tace wannan magana kagece kawai aka mata "Karyace, karyace, karyace", kuma tayi kira ga masoyanta da su watsa wannan karyata labari da tayi dan a wanketa daga zargi.

No comments:

Post a Comment

Pages