
AN TSINCI GAWAR WANI YARO WANDA AKA YI GARKUWA DA SHI A KANO
...ana zargin mijin yayarsa da laifin kashe shi
DAGA AMINU ABDU BAKA NOMA KANO
Lamarin dai ya faru ne a Unguwar Dabai inda aka ga gawar yaran mai suna Usman Dan shekaru shida. Inda aka kwana biyar ana nemansa amma bisa kokarin jami'an tsaran DSS suka gano wanda ake zargi mai suna Abubakar Maikudi. Wanda kuma miji ne ga yayar marigayin.
Tuni dai an cafke wadanda ake zargi da aikata wannan danyan aikin.
Tunda fari dai an dauke yaron ne bayan taso su daga makaranta, daga bisani suka nemi naira miliyan biyu a matsayin kudin fansa, shi kuma yaron ya gane mijin yarsa shine sanadin kashe shi kamar yadda ake zargi.
No comments:
Post a Comment