A jiya Talata, majalisar jahar Ebonyi ta dakatar da daya daga cikin mambobin ta mai suna Misis Maria Ude Nwachi akan laifin rashin da’a.
Rashin da’ar da Nwachi ta aikata dai shi ne kasancewa mai daukan hoto duk da cewa ta na matsayin ‘yar majalisa.
Shugaban majalisar, Hon. Joseph Nwobasi shi ya gabatar da kudirin dakatar da ita, wanda kuma majalisar ta amince da shi.
Majalisar ta ce kasancewa Nwachi mai daukan hoto a jahar abun kunya ne ga majalisar. Majalisar dai ta sha gargadin Nwachi game da wannan batu, a don haka a wannan karon aka dakatar da ita na tsahon kwanaki 14 domin a yi abincke game da batun.
Wannan kuma ba shi ne karon farko da aka dakatar da Nwachi ba.a majalisar.
A shekarar 2016, an dakatar da ita na tsahon fiye da watanni biyu bayan da ta shirya zanga zanga kalubalantar rashin wutar lantarki a yankin da ta ke wakilta, wanda ya haifar da kone konen motoci.
No comments:
Post a Comment