Saturday, January 27, 2018

An Cafke Matashin Da Ya Mayar Da Mutum Bakin Akuya



Hausa_Akuya_Labarai_Alummata_Mayar_Akuya_Bakin_ sanda_Ribas_Jihar Rundunar ‘yan sanda na reshen jihar Ribas na gudunar da bincike a kan wani matashi dan shekaru 36 wanda ake zargi yayi amfani da asiri wajen mayar da wani mutum akuwa.
Rahoton daga kafafen yada labarai na DailyPost sun bayyana cewa ‘yan sanda sun cafke wani mutum dan asalin karamar hukumar Etche wanda wata bakar akuwa ke bin shi a baya a ta yankin kauyen Rukpoku da ke karkashin karamar hukumar Obio-Akpor.
Matashin dan shekaru 36 wanda ‘yan sanda ba su bayyana sunan sa ana zargin sa da rikidar da wani mutum zuwa wata bakar akuya wanda hakan ya sa matasa da ke zama a yankin suka masa dukar tsiya don ya dawo da akuyar zuwa mutum.
Sun masa dukan tsiya har sai da ya suma a nan take.
Sai da jami’ab tsaro masu gudunar da ayyukar tsaro a wannan lokacin suka shiga tsakanin lamarin, idan ba hakan ba da matashin ya rasa ran sa.
‘Yan sanda sun dauki matashin tare da bakar akuyar zuwa ofishin ‘yan sanda da ke Rumuokora inda matashin ya farfado daga suman da yayi kafin ya bayyanawa ‘yan sanda abunda ke faruwa tare da shi da dabbarsa.
“Ina fitowa daga gida na ne sai na gano cewa ashe akuya na na bi na a baya. Dama ta saba bi na a baya a duk lokacin da zan fita saboda ni kan siye mata biskit amma a wannan lokacin ba siye ma ta ba, shine sai na yanke hukunci bare da gudu don na tsere ma ta. Sunan ita wannan akuyar “Remember” wato ” tunawa ko tuni”.
“Abun ya ba ni mamaki da mutane suka aza na mayar da mutum akuyi ne. Ya hakan zai iya faruwa?” ya fadi a cikin mamaki. A yanzu haka wanda aka yiwa dukan, dakuyar tare da wasu matasa 2 daga cikin matasan da suka wa mutumin dukan tsiya suna ofishin ‘yan sanda.
Shugaba ‘yan sanda na ofishin ‘yan sandan Rumuokoro ya ce jami’an tsaro na ‘yan sanda sun fara gudunar game da lamarin don gane gaskiyan al’amarin.

No comments:

Post a Comment

Pages