- Ya gargadi Shekau a kan amfani da yara mata wajen tashin bamabamai
- Ya ce Shekau na azabtar da yaran da yake kamawa kafin daga bisani ya yi amfani da su wajen aikinsa na ta'addanci
Wani kwamandan kungiyar Boko Haram, Abdulkadir Abubakar, da jami'an sojin Najeriya suka damke a Buni yadi dake jihar Yobe tun watan Yuni ya gargadi shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, da ya daina amfani da yara mata da basu san komai ba wajen tayar da hankalin jama'a.
Abubakar da aka fi sani da Abu Muhammad, ya yi wannan kira ne daga ofishin sojin Najeriya dake Maiduguri inda aka garkame shi tun bayan kama shi. Kafin kamun nasa a watan Yuni, Abubakar shi ne kwamandan kungiyar Boko Haram me kula da harkokin samar da bayanan sirri ga kungiyar. Hakazalika ya bayyana cewar baya jin dadin amfanin da kungiyar ke yi da yaran wajen tashin bamabamai.
Abubakar ya kara da cewa Shekau na azabtar da yaran kafin daga bisani ya yi amfani da su wajen aikinsa na ta'addanci a saboda haka ya bukaci shugaban kungiyar da ragowar mukarrabansa da su ajiye makamansu su daina kashe mutanen da basu ji ba balle gani.
"Ina kira ga Abubakar Shekau, Mamman Noor, Abbor Minok, da Abu Musad Albarnawi da su tuba su daina abinda suke yi na kisa babu dalili. Kun kashe rayuka da dama, ya kamata ku ajiye makaman ku, ku tuba. " A kalaman Abdulkadir.
Abdulkadir ya ce a idon Shekau dakarunsa ke aikata fyade ba tare da ko sau daya ya taba tsawatar masu ba, ga yunwa da yake barin yara da matan da ya kama da ita. Yara da dama sun mutu saboda yunwa.
Tsohon kwamandan ya ce kafin a kama shi, shi da ragowar wasu kwamandojin kungiyar da suka bar sansanin Shekau saboda rashin tausayinsa, suna nemansa su kashe shi kamar yadda sojin Najeriya ke farautar sa.
Daga karshe Abubakar ya rufe da cewar; " Ina so Shekau ya sani cewar yaran da yake kamawa yake kashewa ta hanyar daura masu bam su kashe wasu jama'ar, 'yan uwanmu ne, iyayenmu ne, kuma basu cancanci mutuwa a wulakance haka ba. Wannan abinda kake yi ya sabawa fadin ALLAH kuma ta sabawa koyarwa addinin Islama."
Daga shafin naijhausa
No comments:
Post a Comment