Sunday, December 10, 2017

Uche Secondus Ya Zama Sabon Shugaban PDP Na Kasa



* Ya Kuma Ba APC Wa'adi * Sauran 'Yan Takarar Sun Nuna Adawa Ga Sakamakon Zaben An kammala zaben shugabannin PDP na kasa inda Uche Secondus ya samu nasarar lashe zaben bayan ya samu kuri'u 2000. Wanda ya biyo bayansa, shi ne dan takarar yankin Yarbawa, Farfesa Tunde Adeniran wanda ya samu kuri'u 230 sai Shugaban Gidan talbijin na AIT, Cif Raymond Dokpesi wanda ya zo na uku inda ya samu kuri'u 66 kacal. Da yake jawabi bayan lashe zaben, Uche Secondus ya bayyana cewa a ranar 28 ga watan Mayu na shekarar 2019 wa'adin mulkin APC zai kawo karshe inda ya nuna bakin ciki kan yadda wasu 'yan PDP su bayar da hadin kai ga APC a zaben 2015. A dayan bangaren kuma, sauran 'yan takarar kujerar shugabancin PDP sun nuna adawa kan sakamakon zaben inda Farfesa Adeniran ya fice daga dandalin da ake zaben, shi kuwa, Raymond Dokpesi ya zargi gwamnoni da murde zaben.

No comments:

Post a Comment

Pages