![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgtzQZm9CnEzRqnGmXcdytc7lNvoZoSwWcL0wJaR-niRjGLfN5MmspdsV5N5q4T7IFNQSINQJ7Oz7LT-yywvtZmznosgCw2lDP1W8Ugisneh8k2-LOH6SjNyAGEL0VnkNGiWmnaIIQ5N_JL/s320/T%2525255D%25252B%252525282%25252529.jpg)
Shaharariyar jarumar finafinan Hausa Nafisa Abdullahi ta fito tayi bayanin ainihin alakar ta da jaruma Rahma Sadau musamman ma a farfajiyar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood duba da yanayin yadda ake yayata cewa dangantaka a tsakanin su tayi tsami. Jarumar dai tayi wannan karin haske a wata hira da aka yi da ita a Weekly Trust jim-kadan bayan ta amshi kyautar ta ta gwarzuwar jaruma a fina-finan Afirika a birnin Landan a kwanan baya inda ta bayyana cewa ita zaune take lafiya da kowane abokin sana’arta. A lokacin da aka tambaye ta Nafisa Abdullahi ko da gaske ne basa ko ga-maciji tsakanin ta da Rahama Sadau, sai ta kada baki tace ita dai gaskiya wannan zargin ba gaskiya bane don kuwa babu wani sabani a tsakanin su yanzu. Jarumar ta kuma bayyana cewa ita Rahma Sadau kanwa ce a wurin ta sannan kuma dukkan su suna yin aiki ne a karkashin kamfani daya don haka ba gaskiya bane ace kuma suna fada da junan su.
No comments:
Post a Comment