A jiya ne Ambasadan Ƙasar Denmark a Nijeriya, Torben Gettermann ya bayyana cewa akwai buƙatar Nijeriya ta fahimci wasu hanyoyin da suka fi dace wa wurin yaƙi da cin hanci, wanda ba za a iya kawar wa a dare ɗaya ba.
Gettermann ya faɗi haka ne a Jihar Legas, inda ya jaddada cewa yaƙi da cin hanci a kowacce ƙasa, ba aikin dare ɗaya ba, ko wani abu da za a iya yi wa rufa ido. Abu ne da ke buƙatar bin matakai da kuma haƙuri. A ta bakinsa, yaƙinna buƙatar fahimta da kuma bayar da haɗin kai daga ‘yan ƙasa.
Ya ce, “Ba yabon kai ba, amma dai tunda ƙasarmu ta Denmark a tsawon shekaru biyar ita ce ƙasa mafi ƙarancin matsalar cin hanci da rashawa a duniya.
Ina so Nijeriya ta san cewa yaƙi da cin hanci fa ba wasa bane, ba kuma wani abu da za a iya yiwa garaje bane. Abu ne da ke buƙatar jajirce wa da sadaukarwa har a iya kawo ƙarshensa.” Inji sa Gettermann ya ce ƙoƙarin da wannan gwamnati ta Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta ke yi na son ganin bayan cin hanci da rashawa zai kai ƙasar ga matakin nasara, amma fa sai ‘yan ƙasar sun gamsu da ƙaurace wa duk wasu ayyukan cin hancin a wuraren ayyukansu da rayuwarsu ma gabaɗaya.
Ambasadan ya yaba wa gwamnatin tarayya da ƙoƙarinta na samar da yanayi mai kyau don a iya gudanar da kasuwanci a faɗin ƙasar. “Kamfanonin Ƙasar Denmark sun bayyana sha’awarsu da kawo kasuwanci a Nijeriya yanzu”. In ji shi Ya ƙarƙare da cewa; “Akwai ban sha’awa yadda gwamnatin Nijeriya ke ƙoƙarta wa a yanzu wurin ganin ta sauƙaƙa yanayin kasuwanci a ƙasar.
“Mu na kan yin ƙoƙarta wa don ganin cewa wasu ƙarin kamfanonin Denmark sun zo Nijeriya don yin kasuwanci. Wanda hakan zai ƙarfafa yanayin kasuwanci a tsakanin ƙasashen namu biyu.” Inji shi
Daga Hausa Leadership
No comments:
Post a Comment