Thursday, November 16, 2017

Yadda Jirgin Saman Farko Ya fara Sauka A Kano, Kaduna Da Maiduguri



.A shafi na 44 zuwa na 46 na littafin Ɓincent Orange “Coningham: An bayar da tarihin Air Marshal Sir Arthur Coningham”, wanda ya tuƙa jirgin sama na farko da ya fara sauka a Nijeriya ranar 1 ga watan Nuwamba,1925.
Tawagar matuƙa jirgin saman ƙarƙashin jagorancin Flight Lt. Coningham, ta taso daga garin Helwan da ke ƙasar Masar zuwa Kano, Kafin isowar jirgin zuwa Nijeriya, ya yi zango a Sudan da ƙasar Injimena, wadda a lokacin ake kiranta Fort Lamy.
Mai karatu biyo mu ka sha labari daga cikin abin da muka tsakuro muku a wannan shahararren littafi wanda ya bayar da labarin yadda mutanen Kano suka shirya gagarumar tarba ga wannan tawaga da ke cikin jirgin wanda aka yi wa laƙabi da DH 9A, da yadda Sarkin Zazzau, Ibrahim Kwasau, ya shirya wasan Polo ga ‘yan tawagar, da kuma yadda Shehun Borno Sanda ya ba su kyautar raguna, a matsayin murnar da suka nuna ta samun wannan ci-gaba.
“Tun a shekara ta 1925, aka fara tunanin yadda za a fara zirga-zirga a aƙashen Afirka ta jirjin sama. Saboda haka, sai ƙasar Faransa da Baljiyan suka tsara yadda za su fara wannan zirga-zirgar tsakaninsu da ƙasashen da suke wa mulkin mallaka. Wannan yunƙuri ne ya zaburar da ƙasar Birtaniya don kar ta bari a bar ta a baya. A ƙoƙarin cim ma wannan buri, a cikin watan Satumba, Ma’aikatar kula da sararin samaniya ta sanar da cewa, jirgin saman DH 9A na runduna ta 47, wanda ke Helwan, kusa da ƙasar Alƙahira zai taso daga can zuwa Kano da ke Nijerya, domin su gwada tafiya nesa da jirgin zuwa ƙasashe masu zafi, waɗanda suke da filin da jirgin zai iya sauka, da kuma manufar ‘yan Nijeriya su ga ƙoƙarin da ƙasar Birtaniyan ke yi na samar da jirgin sama.
“Shugaban rundunar sojan sama Coningham ne ya jagoranci tawagar a kan wanna tafiya. Babbar matsalar da suka fara cin karo da ita ita ce, ta sadarwa da kuma injin jirgin. Kodayake akwai tashar watsa saƙwanni a kan hanya, sai dai a cikin jirgin babau na’urar da ke iya watsa saƙo ko karɓarsa, sai dai kawai su yi amfani alƙibla ko taswira, wanda kusan za iya cewa, ba su da amfani. Ƙarfin injin jirgin bai wuce 400 hp, saboda haka sai ya zama ba ya iya samar da saƙon da yake da sahihancin da za a dogara da shi, sakamakon haka sai matuƙin jirgin Coningham ya rage gudun jirgin na DH 9A, wanda aka tsara zai yi tafiyar 90 mph zuwa 80 mph. “Jirgin ya tashi daga ƙasar Helwan Ranar 27, ga Oktoba da misalign ƙarfe 7ns, tawagar na ɗaga wa taron sojojin ƙasa da na samu don yin ban-kwana, Sun fara sauka a garin Wadi Haifa, da ke da nisan mil 644 kudu da garin Helwan bayan sun shafe awa takwas da minti ashirin suna tafiya a sararin samaniya, Dukkan matuƙa jirgin su uku da ke cikin tawagar sun ɗaura bel a kafaɗunsu da kuma ƙirjinsu, don gudun kada jirgin ya tashi su rinjaya zuwa jelar jirgin kamar yadda matuƙin jirgin Coningham ke cewa, ya kamata su daidaita, saboda ya ce ya ji kamar nauyin nasu na neman rinjaya.
Tashin nasu na farko shi ne wanda suka fi yin tafiya mai nisa, kuma suka fi shan wahala a dukkan tafiyar da suka yi wadda suka keta sararin samaniya sau goma sha shida. Bayan direban jirgin Wadi Haifa, Coningham ya rage yawan kayan da jirgin ya ɗauko, ya tashi da misalig ƙarfe 4.50ns zuwa Kartum inda suka isa da rana. Tafiyar ta yi sauri sosai saboda rage yawan kayan da aka yi, sannan kuma sun samu sake wa sosai a cikin jirgin.
“Manuniya ta nuna cewa, in ya yi yamma zai je garin, yana kaɗa akalar jirgin sai ya ga wasu jerin tsaunuka, waɗanda bai gansu a cikin taswirarsa ba. Saboda haka, sai ya yi tunanin cewa, garin na El Fasher na gabas da waɗannan tsaunuka, sai ya kauce musu, ya kuma ci gaba da tafiya, inda ya sake nuna masa wani tsaunin da ke da nisan mil ashirin da biyar ta yamma. Bayan kimanin minti goma shabiyar, sai ya hangi garin, nan suka sauka lafiya, duk da tayar jirgin ta samu matsala, nan suka sauka, suka huta. Bayan sun ƙara mai sai suka ci gaba da tafiya da taimakon sauran matuƙan da ke cikin jirgin. Lokacin da suka sauka a El Fasher ne Coningham ya ɗauki cutar maleriyar da ta naƙasa shi har zuwa ƙarshen rayuwarsa. “‘tun daga wannan lokaci ne garin bai sake ganin wani jirgin sama ya sauka ba, sadoda kallaon da ake yi wa garin na El Fashe a mtsayin garin da ke da annoba, Sannan kuma yamma da garin ana kunna wuta da gangan wadda hayaƙinta ke turniƙe sararin samaniyar da ya kai kimanin nisan ƙafa 4,000, saboda haka duk jirgin da ya ratsa garin bisa rashin sani zai ga hayaƙi na fito wa daga injinsa kamar wani abu na ƙone wa, har sai ya samu tabbacin cewa, babu abin da ke ƙone wa, hayaƙi ne daga ƙasa. Bayan sun bar El Fasher, sai suka bi wata hanya da raƙuma ke bi, lokacin da Musulmi ke tafiya Maka domin yin aikin Haji, har zuwa inda suka shiga ƙasashen da ke da yawan tsaunuka. Bayan sun sauka a garin Abecher, da daddare, daga nan sai suka tashi zuwa ƙasar Fort Lamy. Daga nan Coningham ya yi niyar kaɗa akalar jirgin zuwa Maidugari, amma sai ya fahimci hayaƙi na fito wa daga cikin jirgin fiye da yadda ya saba gani, saboda haka sai ya yanke shawarar koma wa Fort Lamy, ya sauka. Bayan saukar ta sa ne ya ga ashe ma fi yawan Man jirgin ne ya zube, wanda da sun ci gaba da tafiya da jirgin ya faɗo a cikin wani daji mai kimanin nisan ƙasa da mil arba’in daga inda suka taso’. Wani lokacin mukan lura da cewa, yana tuna wannan abin da ya so ya faru.
“Kashegari da misalig ƙarfe 10.20ns suka tashi zuwa ƙasar Fort Lamy da wasu ƙasashen rainon Faransa zuwa wasu da ke ƙaraƙashin rainon Turawan Ingila. Labarin saukar jirgin na bazuwa al’umma suka fito inda suka yi dafifi a kan hanyar Maiduguri zuwa Kano, kowa ya ɗaga kansa sama yana jiran ya ga jirgin da aka ce ya iso ƙasar nan, ya rubuta a cikin littafin cewa, ‘mutane sun dandazo a kan hanya waɗanda suka fito daga lungu da saƙo na garuruwan.’yayin da jirgin ya sauka matuƙin jirgin Coningham ya nemi afuwar jama’a sakamakon jinkirin da ya samu, maimakon sauka jiya da daddare, sai yanzu da gari yawaye, sannan auka sauka. Ya ce, hakan ta faru ne sakamakon matsalar da injin jirgin ya samu, wanda sai da ya shafe kimanin minti arba’in da biyar kafin ya shawo kansa, saboda ya sauka agurin da yake da rairayi, kuma rairayin ya shiga cikin injin jirgin, kafin ya yi dabarar sauka a wannan fili na polo da ke da ƙasa mai tsauri.
Saboda haka ne ma jirgin ya samu matsala a wannan lokaci, matsalar da ba mu samu ba a tsawon lokacin da muka yi muna tafiya na tsawon awa ashirin a sararin samaniya. “An sa ran jirgin ya isa Kano da misalig ƙarfe 10.00ns, da kuma mun yi hakan amma saboda matsalar kafireto da muka samu hakan ba ta yi wu ba. Wakilan gwamnan Legas da suka zo Kano domin taryar jirgin sun gaya wa dandazon jama’ar da suka taru cewa, jirgin zai sauka da misalin ƙarfe 5ny. Matuƙin jirgin Coningham ya cika wannan alƙawarin, domin kuwa ya sauka a filin polo da ke wajen cikin garain Kano da misalin ƙarfe 5.10ny ranar 1, Nuwamba, 1925, bayan kwana shida da tasowarsa. Daga nan hankalin jama’a ya kwanta domin abin da suka daɗe suna jira ya iso, sannan suka gaya wa Coningham sun ji abin da ya faru. Tsayawar jirgin ke da wuya sai aka sa igiya aka kewaye shi don gudun kada turereniyar jama’ar da suka taru su yi ɓarna a jirgin. Saboda haka dukkan mutanen da suka zo taren jirgin su sama da mutum dubu ashirin(20,000) suka tsaya a bayan fili suna hangen jirgin. Masu kula da saukar jirgin sun nuna cewa, nisan daga inda jirgin ya taso watau, Helwan ya kai kimanin mil 2,904, wanda suka yi tafiyar cikin awa talatin da shida da minti arba’in, sai dai haƙiƙanin tafiyar da jirgin ya yi kafin ya iso wannan guri ta kai ta sama da mil 3,000 a tafiyar da yake ta 83 mph.
“A duk tsawon tafiyar da suka yi, Coningham ya lura da cewa, ƙasashe kaɗan ne ke da filin saukar jirgi maikyau, kuma tsakaninsu akwai nisa. Nisa da lokacin da daɗewar da za a yi kafin a je irin waɗannan gurare ya sa shi dogon tunani. Ya ce, misali idan aka samu matsala a kusa da wani tabki da ake kira Fittri, dole matuƙa jirgin su zauna, ba abinci sai dai ko naman dajin da suka harba ko kuma abin da za su saya daga gurin mutanen ƙauyen, har sa an kawo musu ɗauki, wanda tafiyar kiman kwana arba’in da biyar ce daga Fort Lamy zuwa Abecher: tafiyar da jirji zai iya yinta a cikin awa biyu da rabi. Babu tabbacin za a iya sauka lafiya-lafiya tsakanin Kaduna da El Obeid, sai wani gari yamma kaɗan da Abecher. Sanin haka sai Coningham ya rubuta, ‘Kasancewarsa wanda ya tuƙo wannan jirgi ya fahimci cewa, tafiya a jirgin sama wani lokacin ta fi rashin sauri. Domin kuwa za ka ga guri mai kimanin nisan ƙafa 3,000 wanda in fili ne za a iya hangensa tun da bai wuce nisan mil 150 ba, amma saboda tsaunuka, sai ka ga sai ka daɗe kafin isa gurin, domin kuwa dole ka tafi a hankali in ba haka ba, ka yi gaggawa ka ƙarasa ɗan injin da kake lallaɓa wa da shi. “Bayan tasowarsu daga Kano mai nisan mil 130 kudu-maso-yamma,, sai suka sauka a garin Kaduna ranar 6 ga watan Nuwamba, inda aka yi wa tawagar matuƙa jirgin kyakkyawar tarba, sannan aka jagorance su zuwa gidan gwamnati, inda aka shirya musu liyafa, nan suka kwana huɗu. Haka aka shirya jama’a suka nuna farin cikinsu da jin daɗin bisa ƙaunar da suka ce an nuna musu ta sake dawo wa ƙasar, an yi kwana biyu ana yin wasan polo’ daga nan Coningham ya ɗauki Sarkin Zazzau da wani sojan sama Laftanar Humphrey Baggs da wasu saja-manja guda biyu ɗaya daga cikinsu Bahaushe ne. Lokacin da ya shiga jirgin sai wani tunani ya zo masa, inda ya fara murmushi, suna fara tafiya sai ya fara rera waƙa cikin tattausar muryarsa har suka sauka yana wannan waƙa mai sanyaya zuciya.
Tawagar matuƙa jergin sun bar Kano zuwa Maidugari a kan hanyarsu ta koma wa gida ranar 12 ga watan Nuwamba da misalin ƙarfe 7ns, inda jirgin ya dinga tafiya ƙasa-ƙasa kimanin nisan ƙafa 1,000, don mutane su samu damar ganinsu sosai da sosai. Isowar su Borno ke da wuya tun da, da ma suna tafiya ƙasa-ƙasa ne, sun ga yana yin ƙasar, ba su sake yarda sun sauka a gurin da yake da rairayi ba, kamar wancan karon wanda ya sa injinsu ya samu matsala, sai dai suka sauka a filin polo. Saboda haka, aka gabatar da tawagar matafiyan ga Sarkin Barno, wanda ya ba jagoran matafiyar Coningham manyan fararen raguna guda biyu, wanda ya yi farin cikin wannan kyauta, sannan ya bayar a ajiye masa har zuwa lokacin da za su tafi.
“Bayan sun yi ban-kwana sun ɗaura ɗamarar koma wa inda suka fito, tafyar ta su ta yi kyau domin ba su ci karo da wata gagarumar matsala ba, sai dai matsalar isaka mai ƙarfi da suka fuskan da kuma faci da suka yi a tayarsu lokacin da suka sauka a gida ranar 19, ga watan Nuwamba 1925. Tawagar da ke ƙarƙashin jaorancin Coningham sun shafe kwana goma sha shida suna tafiya a sararin samaniya, daga cikin kwana ashirin da huɗu da suka yi a tsawon tafiyar ta su. Tafiyar da aka ƙiyasta ta kai ta nisan mil dubu shida da ɗari biya(6,500). Haka kuma tafiyar sun shafe awa tamanin suna tafiya a sararin samaniya, sun samu matsala a cikin injin jirgin har sau uku. Tawagar ta ji daɗin tafiyar saboda, zaman awa hansin da uku da suka yi cikin farin ciki a wasu ƙasashen da ake ganin shigarsu zai yi wuya.Ma’aikatar kula da sararin sama na alfahari da abubuwa guda biyu: A bu na farko shi ne, keta ƙasashen Afirka ta sama da kuma saukar jirgin sama na farko a Nijeriya, tafiyar da aka saba yinta a jirgin ƙasa da raƙuma da kuma shanu wadda ke ɗaukan kimanin wata shida.
Bayan saukar wannan jirgin sama na farko mutanen Kano ba su sake ganin wani girji ba, sai bayan shekara goma inda jirgin Imperial Airways ya sauka lokacin Sarkin Kano Abdullahi Bayero a shekara ta 1935.
An bayyana ɓacewar Coningham ranar 30 ga watan Janairu na shekara ta1948, lokaci ya tuƙa wani jirgi G-AHNP wanda ya yi ƙoƙarin keta hatsabibin yankin nan mai suna Bermuda, wanda tun daga wannan lokaci aka neme shi aka rasa, saboda haka aka bayar da sanarwar mutuwarsa. Coningham, gwarzo ne wanda tarihin tuƙin jirgi sama ba zai cika ba, sai an Ambato sunansa. Har ya zuwa wannan lokaci dai ba iya gano gawarsa ba, domin inda yahalakan babu mai iya leƙa wa gurin sai dai kwatance.

No comments:

Post a Comment

Pages