Sati biyu kenan da yin auren na su amma har ta gundura da angon na ta - Amaryar ta ce shi ne ke yin dukkan aikace-aikacen gida, sam ya hana ta taimakawa - Angon na ta ya ce mata dole ne ta bi ka'idojin sa idan har ta na son cigaba da zaman gidan Wata mata mai suna Samar, mai shekaru 28 kuma 'yar Kasar Egypt, ta nemi mijin ta, Mohammad S., mai shekaru 41 da ya sake ta, makwannai 2 kacal bayan auren su.
Kamar yadda Jaridar Punch ta wallafa, matar ta nemi sakin ne saboda yadda mijin ta ke yin dukkan aikace-aikacen gida, irin wanda matar gida ce ya kamata ta rinka yin su, ya kuma ki barin ta ta taimaka ko kadan.
Ta ce yayin da ta fuskance shi da damuwar ta, sai ya ce mata dole ne ta bi dokokin sa idan har ta na son ta cigaba da zaman gidan ba domin ita a ganin ta ya maida kanshi matan gida ba ita ba.
Shi dai mijin na ta yana da shagon sayar da kaya ne, ya na kuma da yara da yawa masu kula masa da shagon. Don haka ne ya ke da isasshen lokaci shantakewa a gida.
No comments:
Post a Comment