Wani mutum ya bukaci kotu ta raba auren sa da matarsa da suka kwashe shekaru 22 tare bisa dalilin rashin dafa masa abinci - Har ila yau, mutumin yayi ikirarin cewa matar bata zama a gida kuma bata yi masa biyaya kwata kwata - Matar tasa itama tace ta gaji da zaman auren sai dai ta roki kotu ta bata izinin rike dan autan su
A ranar Alhamis ne wani dan kasuwa mai suna Garbar Pakaci mai shekaru 45 a duniya ya nemi wata kotu a garin Abuja ta raba aurensa da matarsa da ya aura shekaru 22 da suka wuce bias dalilin rashin dafa abinci da bata yi a kullum.
A takardar neman raba auren da Pakaci ya shigar a Kotu, yayi ikirarin cewa tun ranar da ya auri matar sa Martha Ahmed ya dena samun kwanciyar hankali a rayuwarsa. Ya kara da cewa bata yi masa biyaya galibi ma sau 1 take dafa abinci a mako.
Pikachi ya kuma ce matar tasa bata zama a gida, sai dai zuwa gidajen rayeraye, wasu lokutan ma bata kwana a gidan sai da safe take dawowa.
Pikachi yace yayi iya kokarinsa wajen ganin cewa matar tasa ta canja halayen ta amma abin yaci tura, hasali ma ya gaji da auren saboda haka yana son kotu ta raba auren kuma ta bashi izinin rike yaransu 4. Matar tasa, Martha Ahmed wadda ta samu hallartan kotun tace itama ta gaji da auren amma ta roki kotu ta bata izinin rike dan autan su.
Alkali mai sauraron karar na Pikachi, Jemilu Jega ya ja kunuwan ma’auratan inda yace zaman aure na shekaru 22 ba wasa bane. Ya kuma shawarce su da suyi kokarin sulhunta kansu kafin ya sake sauraron karar a ranar 21 ga watan Nuwambar 2017.
No comments:
Post a Comment