Monday, November 20, 2017

Wallahi ko kadan ban yi niyyar kashe masoyina uban 'yata ba - Inji Maryam Sanda



A cewarta ba tayi niyar kashe uban yar ta ba - Ta kuma daura abun akan sharin shaidan Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa matar dan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, kuma tsohon ministan tsaro, Bilyamin Muhammed Bello ta sanar da cewa ko kadan ba niyarta ne kashe mai gidan nata ba.
A cewar Maryam Sanda hakan da ta aikata ba komai bane face sharrin shaidan. Ta ce: “Wallahi ko kadan ban yi niyyar kashe masoyina uban 'yata ba, sharrin shaidan ne.”
Idan zaku tuna NAIJ.com ta ruwaito a bayan cewa Bilyamin Muhammed Bello ya gamu da ajalinsa a hannun matarsa ta sunnah.
Hakan ya faru ne ya faru ne sakamakon zargin yana tarayya da wata budurwa ta daban da matar tasa ke yi ne, inda da fari sai ta fara cizan masa kunne, kuma yayi jinya a asibiti bayan an dinke kunnen.
Rahotannin sun bayyana cewa abokansa sun bashi shawarar daya bar gidan, amma ina, ajali yayi kira, a daren Asabar, 18 ga watan Nuwamba ne, Maryan ta sadada dakinsa dauke da wuka, bayan tag a wani wasikar kar-ta-kwana a wayansa daga wata budurwa, inda ta mamaye shi ta caccaka masa a baya, sa’annan ta sossoka masa a al’auransa.

No comments:

Post a Comment

Pages