Monday, November 20, 2017

Takaitaccen tarihin Abubakar Tafawa Balewa



An haifi Sir Abubakar Tafawa Balewa a garin Tafawa Balewa dake jihar Bauchi a Arewa maso Gabashin Najeriya a shekarar 1912.
Ya kasance mutum mai da'a da kuma asali kasancewar mahaifinsa ma'aikaci ne ga hakimin garin.
Yayi karatu a makarantar horon malamai ta Katsina daga ( 1928 zuwa 1933), sannan ya zamo malami, kuma shugaban makarantar Bauchi Middle School.
Yayi karatu a makarantar horas da malamai ta London daga ( 1945 zuwa 1946), inda ya samu shaidar malanta.
A lokacin yakin duniya na biyu ya nuna sha'awarsa ta shiga harkokin siyasa, inda ya kafa zauren tattaunawa na Bauchi Discussion Circle.
Sannan daga bisani ya shiga siyasar malamai inda aka zabe shi mataimakin shugaban kungiyar malaman Arewa.
A shekarar 1952 ya zamo ministan ayyuka na Najeriya, ministan sufuri a 1954, sannan ya zamo jagoran jam'iyyar NPC a majalisar wakilai ta kasa.
Ya zamo Fira Ministan farko na Najeriya bayan da kasar ta samu 'yancin kai a shekarar 1960. A shekarar 1966, wasu sojoji suka yi kokarin juyin mulki inda anan ne aka sace shi kafin daga bisani aka kashe marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa.

No comments:

Post a Comment

Pages