Rundunar tsaro na musamman da ake wa taken ‘Operation Sure Haɓen’ sun yi nasarar cafke wasu Mata a ranar Talata, bisa tuhumar su da laifin safarar ƙaramar Yarinya mai shekaru 4 kacal da haihuwa.
Waɗanda ake tuhumar sun haɗa da Egbufurum mai shekarun haihuwa 39, da kuma Esther James mai shekarun haihuwa 40 an kama su ne ɗauke da Yarinyar a daidai shingen binciken ababen hawa na jami’an tsaro da ke Babale Gwam wanda yake kan iyakar Jihar Bauchi da Plateau. Kwamandan rundunar Sojin da ke ‘Sector 1’ kanar Musa Etsu-Ndagi wanda shi ya gabatar wa manema labarai da waɗanda ake tuhumar, ya bayyana cewa, an kama su ne da misalin ƙarfe 7:15 na yamma a ranar litinin, a daidai shingen binciken ababen hawa, bayan da suka shigo wata Motar haya daga garin Bauchi. Ya bayyana cewa, “Ɗaya daga cikin Fasinjojin da ke cikin Motar ce ta ankarar da jami’an tsaro, inda ta bayyana musu cewa ta na zargin Matan sun sato Yarinyar ne, saboda babu wata alama da ta nuna cewa a cikin su akwai Mahaifiyar Yarinyar, sai jami’an mu suka kame su, da aka gudanar da bincike, sai ta bayyana cewa siyo Yarinyar su ka yi daga garin Bauchi daga wurin wani mai suna Mr. Abuna a kan Kuɗi dubu 300,000.
Ya bayyana cewa, Yarinyar yanzu haka tana hannun rundunar na Soji, inda aka damƙa ta a hannun sashen da ke kula da lafiyar Sojoji suna ci gaba da ba ta kyakkyawar kulawa. Etsu-Ndagi ya ƙara da cewa, rundunar OPSH tana ƙoƙarin mayar da Yarinyar ga hukumar gwamnatin tarayya da ke yaƙi da safarar Mutane (NAPTIP) wanda ke ƙarƙashin ma’aikatar shari’a ta tarayya. Ya jaddada cewa hukumar ta NAPTIP ba su da Ofishi a Jihar ta Plateau, Ofishin su mafi kusa shine wanda yake garin Makurdi da ke Jihar Benue.
Ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhumar, Egbufurum, wacce ‘yar asalin Jihar Imo ce, amma take aikin nas a Asibitin ‘Peoples Clinic’ da ke garin na Bauchi, ta bayyana cewa, tana kan hanyar ta ne na kai Yarinyar Garin Lagos, bayan da ta saye ta daga hannun wani da suka saba hulɗar sayayya da shi a garin na Bauchi.
“Ina kan hanya ta na kai Yarinyar ga wata Mata ce da ta daɗe da yin aure, amma ba ta samu haihuwa ba, dubu320,000 ta turo mini dan yin cinikayyar, ni kuma a kan dubu300,000 na sayi Yarinyar, inda na yi niyyar yin anfani da ragowar dubu20,000 ɗin da yayi saura dan yin Kuɗin sufuri daga garin Bauchi zuwa Lagos, inda zan kai mata Yarinyar”. Yayin da mu ka tuntuɓe shi, mai magana da yawun rundunar OPSH, Kaftin Umar Adams, ya bayyana mana cewa, za su miƙa waɗanda su ke tuhumar zuwa ga hukumar NAPTIP.
Ya bayyana cewa, “ Rundunar mu sun tsare wata Mota wacce take ɗauke da Fasinjoji, Fasinjojin da ke cikin Motar ne su ka ankarar da rundunar mu, inda rundunar namu su ka yi nasarar gano Matan guda 2 ɗauke da Yarinyar da ake zargin sato ta su ka yi, sai muka kame su, inda mu ka wuce da su cibiyar mu”. “Sun taho ne daga garin Bauchi, a yayin da suke amsa tanbayoyin mu, sai suka bayyana cewa siyo Yarinyar su ka yi, za mu damƙa su ga hukumar NAPTIP domin ɗaukan matakan Shari’a, sannan a yanzu haka muna bakin ƙoƙarin mu dan gano wurin da su ka ce a can su ka siyo Yarinyar”.
No comments:
Post a Comment