Tuesday, November 21, 2017

Sabon rikici tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU game da kwangen Naira biliyan 5


Sabon rikici na shirin sake kunno kai a tsakanin gwamnatin shugaba Buhari ta tarayya da kuma kungiyar malaman jami'oi na ASUU saboda zargin kwange wajen basu kudun su da suka kai akalla Naira biliyan 5. Wannan alamu dai na kunnowar rikicin mun same shi ne jim kadan bayan kammala wani babban muhimmin taro na masu ruwa da tsaki na majalisar zartarwar kungiyar a satin da ya gabata a Abuja babban birnin tarayya.

Majiyarmu dai ta samu cewa kungiyar ta ASUU tuni har ta kafa wani kwakkwaran kwamiti da zai shawarce ta game da yadda zata bullowa lamarin a dukkan rashinan kungiyar dake a jami'oin tarayyar kasar nan. Tun farko dai abun da ake kyautata zaton ya jawo wannan badakalar shine zargin da gwamnatin tarayya ke yi ma kungiyar ta ASUU na rashin biyan kudin haraji a kasa, zargin da su kuma kungiyar suka karyata da cewa su ba kasuwanci suke yi ba.

No comments:

Post a Comment

Pages