Leonardo DaVinci, mai zane-zane da falsafa da kimiyya, wanda ya rayu a Italiya, kimanin shekaru 500 da suka shude, ya bar manyan zanunnuka na Yesu, da Kiristanci, da sahabbansa, da ma na mata haka a gari, kamar na Mona Lisa ko kuma Madonna, wata mata mai murmushi da hotonta yafi kowanne zane a duniya tsada.
A gwanjon hotuna na tarihi masu muhimmanci ga mutane, an sayar da hoton Yesu Al-Masihu a farashin da ya kai dala miliyan 400, kwatankwacin Naira miliyan dubu dari har da hamsin kenan. Kudin bajat din jiha kenan a Najeriya.
Shi dai Yesu, a fadin wasu jama'ar, ya rayu ne a cikin Yahudawa, da ga wani Kafinta mai suna Yusufu, da matarsa Maryamu, wadda daga baya ake cewa ai ma wai shi dan wani ubangiji ne da ke zama a sama.
Wannan yasa ake son shi Yesun har ma shi Leo da Vinci ya zana hotonsa da ma na sahabbansa, wanda a yanzu masoya ke rububin saya domin tubarraki.
No comments:
Post a Comment