Matasan sun bayyana cewar saida suka aikewa Sanatan takardar gargadin kada ya sake ya zo jihar domin yin zaben kananun hukumom dake gudana yau .
Gidan da matasan suka kone a daren jiya juma'a an bayyana cewar mallakar Sanatan dake wakiltar jihar Kwara ta arewa ne, Shaba Lafiagi, bisa zargin rashin tabuka wani abin kirki ga jama'ar yankin na sa.
Majiyar mu ta bayyana mana cewar Sanata Lafiagi ya isa mahaifar ta sa da misalin karfe 8 na daren juma'a tare da rakiyar dumbin jami'an tsaro amma duk da haka fusatattun matasan suka yi kokarin hana Sanatan Shiga garin, dalilin da ya yi sanadin rasa ran wasu matasan su biyu tare a jikkata da dama bayan 'yan sanda sun bude wuta kan matsan.
Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Kwara, Mista Ajayi Okasanmi, bai tabbatar da faruwar hakan ba.
Wata majiya ta shaidawa gidan talabijin na Channels rikicin ya samo asali ne saboda cushen dan takara da matasan suke zargin Sanatan da yi. Ana cikin halin zulumi yanzu haka a garin na Lafiagi dalilin da ya tilasta mazauna garin zama cikin gidajen su domin gujewa kamun 'yan sanda idan suka fita kada kuri'a a wurin zaben na yau.
No comments:
Post a Comment