Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya yi raddi ga tsohon Gwamnan Legas, Bola Tinibu wanda ya yi ikirarin cewa a zamanin Mulkin Jonathan an rika satar kudaden gwamnati na fitar hankali ta yadda har gwamnatin sa ta samu yabo kan yayata rashawa. Da yake raddin, Jonathan ya nuna cewa gwamnatinsa ta samu Tagomashi daga kungiyar kasa da kasa kan yaki da rashawa inda Nijeriya ta matsa daga kasa ta 144 zuwa 136 a cikin wadanda ke yaki da rashawa. Ya kara da cewa har yanzu babu wanda ya fito ya karyata ikirarin da ya yi a shekarar 2014 kan cewa ba shi da asusun ajiyar banki ta kasar waje.

No comments:
Post a Comment