Sule Lamido mutum ne wanda ya cancanci a ce ya jagoranci talakawan Nijeriya. Domin a kullum ba shi da wani tunani illa yadda zai tallafawa Talakawansa. Haka kuma ba shi da wani buri illa ya ga ya dawo da tattalin arzikin kasar nan. Shi bai ce ya fi kowa ba kuma bai kira kansa da mai gaskiya ba. Sannan kuma ba ya alkawarin abin da ya san ba zai iya ba. Dan halak kadai a Jigawa zai iya yi masa wannan shaidar kuma ni bana tantama ko shakkar cewa idan Allah ya baiwa Lamido mulkin kasar nan Talakawa za su wahalta, domin shi mutum ne mai tausayi da sanin ya kamata.
No comments:
Post a Comment