Rundunar Yansandan jihar Kano tayi bajakolin wasu matasa su Uku da take zargi da hannu cikin satar kananan yara a cikin garin Kano, inji rahoton Premium times. Kaakakin rundunar, DSP Magaji Musa Maji yace barayin sun bukaci a biyasu kudin fansan yaran ne ta hanyar tura musu katin waya, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.
Majia yace sai dai yayin da ake cinikin kudin fansa tsakanin iyayen yaran da barayin, sai kuma su dauke su kais u wata uwa duniya, kamar garin Gwarzo, inda suke bayyana yaran a matsayin wadanda suka bata kuma ake neman iyayensu ga dakacin garin.
“Haka suke matsa lamba ga iyayen yaran har sai sun tura musu katin waya a matsayin kudaden fansa, zuwa yanzu cikin yara bakwai da suka sata, iyayen yara hudu sun tura musu da katin da ya haura sama da dubu dari.” Inji Majia. Daga karshe, an ceto yaran gaba daya su bakwai, inda aka gano wayar hannu guda daya, layukan waya uku, da kuma katin waya.
Daga cikin miyagun mutanen, Khalifa Usman yace suna kai yaran wajen mai unguwa ne domin basu da wajen ajiye su. Allah ya shiga tsakanin Nagari da mugu.
No comments:
Post a Comment