Wednesday, November 15, 2017

A Taimaka A Raba Aurena Da Mijina, Mazaƙutarsa A Mace Take – Wata Mace Ta Faɗawa Kotu



Wata mace ‘yar shekaru 32 ta rankaya kotu, inda ta nemi kotu da ta raba aurenta na shekaru huɗu da mijinta bisa matacciyar mazaƙuta da ta ce mijin nata na ɗauke da ita Wannan mace mai suna Kate Ude, ta gurfanar da mijinta, Michael Ude a gaban babban kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a unguwar Jabi a birnin tarayya, Abuja, inda ta shaidawa kotu cewa duk a tsawon shekaru hudun da suka kasance tare a matsayin miji da mata, sai ta yi namijin kokari kafin al’aurar mijin nata ya miƙe, kuma da zarar sun fara tarawa, baya wuce ‘yan sakanni mijinta ya ke kawo Kate ta bayyanawa kotu cewa Michael bai sanar da ita yana da matsalar lafiya ba kafin a daura aurensu a shekarar 2014 a garin Calabar, babban birnin jihar Cross River Kate ta ci gaba da cewa, ko a ranar da aka daura aurensu na gargajiya da Michael bai zo wajen daurin auren ba, sai kaninsa ne ya wakilce shi A lokacin da ya ke mayar da martani ga kotu, Michael ya ce ba a koda wane lokaci bane al’aurarsa ke kin tashi, sai dai kawi shi ba mutum bane mai yawa sha’awa kuma baya shan magungunan karfin maza Michael ya ci gaba da cewa akwai lokacin da matarsa, Kate ta bar gidansa akan wai ta gaji da aure tun a farkon aurensu, sai daga baya ta dawo kafin ta sake yin irin wannan tafiyar Mai shari’a Venda ya dage sauraren karar zuwa ranar 6 ga watan Fabrairun, 2018

No comments:

Post a Comment

Pages