
- Ta ba da hakurin ne kan yanayin da ta fito a wani bidiyon waka wanda yayi sanadiyar koranta daga masana’antan Kannywood - Jarumar ta yi alkawarin cewa irin haka ba zai sake faruwa ba - A shekarar bara ne aka dakatar da Rahma daga masana’antar shirya fina-finan Hausa Daga karshe korarriyar jarumar Kannywood Rahama Sadau ta ba gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II hakuri. Jarumar ta bayar da hakuri ne a kan yanayin da ta fito a wani bidiyon waka wanda yayi sanadiyar koranta daga masana’antan Kannywood a shekarar da ta gabata. A daren ranar Talata, 24 ga watan Oktoba, da take magana a wani shirin gidan radiyo mai taken “Ku Karkade Kunnuwan Ku” wanda ake gabatarwa a shahararren gidan radiyo a garin Kano, Radio Rahama, jarumar ta sha alwashin cewa irin haka ba zai sake faruwa ba. A shekarar bara ne dai aka dakatar da jaruma Rahama daga masana'antan shirya fina-finan Hausa bayan bayyana da tayi a cikin wani bidiyon waka na wani makakin Arewa wanda ake ganin bai dace ba, sannan cewa ya saba ma dokar Kannywood.
No comments:
Post a Comment