Saturday, October 7, 2017

Karya ne Buhari bai samar da tsaro ba a Borno - Buba Galadima


Fitaccen dan siyasar nan kuma jigo a jam'iyya mai mulki ta APC Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa shi bai yadda da karairayin da ake ta yi ba na cewa wai an samu zaman lafiya a Maiduguri don kuwa duk labarin kanzon kurege ne. Injiniya Buba Galadima da a 'yan kwanakin nan sunan sa ke ta yawo a kafafen yada labarai na cikin gida Najeriya ya bayyana cewa har yanzu babu cikakken tsaro a jihar Borno kamar yadda ake ta yamadidi a cikin gari.

KARANTA:- Jam'iyyar APC Ba Ta Cancanci Zama jam'iyya Ba — Inji Buba Galadima


Majiyarmu ta samu cewa shahararren dan siyasar ya kuma ce zai yadda da maganar samar da tsaron ne a jihar idan har mutane za su iya daukar mota su tuka daga duk inda suke su je wasu garuruwan dake a cikin jihar ta Borno irin su Baga da Chibok da dai sauran su. A kwanan baya dai mai karatu zai iya tuna cewa Buba Galadima ya shaidawa majiyar mu ta BBC Hausa cewa idan da shine shugaban INEC da tuni ya wargaza jam'iyyar APC don kuwa ta karya sharuddan kafa ta.

-naijhausa

1 comment:

  1. Enter your comment...karya kake tsoho kaje gd kafuta.bb buhari sai ta allah

    ReplyDelete

Pages