Yan bindigar sun budewa al'ummar wuta dake yankin kasuwar Abraka na unguwar Cable point, baya ga haka kuma suka jefa bam cikin wani masallaci. Jaridar VANGUARD ta ruwaito cewa, wani bahaushe ya yi ta maza yayin da ya dauki bam din da hannunsa kuma ya jefa shi cikin wani kogi tun kafin ya fashe. Rahotanni daga shafin DAILY POST sun bayyana cewa, dakarun soji da jami'an 'yan sanda ne suka garzaya da wadanda suka samu rauni zuwa asibiti bayan sun kwantar da tarzomar.
No comments:
Post a Comment