Wani asibiti a tsakiyar China yana nazari kan yadda aka yi har wata mai tsohon ciki da ke nakuda ta kashe kanta. Likitocin matar sun shawarci danginta a kan su bari a yi mata tiyata saboda lokacin haihuwarta bai yi ba, kuma kan jaririnta ya yi girma da yawa amma sai suka ki. Kafar yada labaran China ta ce mijin matar ne ke son ya ga mai dakinsa ta haihu da kanta maimakon yi mata aiki. Sai dai mai nakudar ta gaza jurewa tsananin ciwo inda ta fado kasa ta tagar asibitin, kuma ta kashe kanta da jaririn da take dauke da shi. Batun ya janyo muhawara a shafukan sada zumuntar China, inda wasu ke tuhuma a kan dokar da ta ce sai dangin mutum sun amince kafin a iya yi masa aiki a asibiti.
No comments:
Post a Comment