Monday, September 4, 2017

Yadda Wani Mahauci Ya Yi Yunkurin Yin Balangu Da Naman Yarinya 'Yar Shekara 4


Rundunar' yan sanda ta jihar Legas ta kama wani mahauci dan Arewa, mai suna Aliyu Abdullahi dake zaune a unguwar Ebute Meta, bisa zargin yunkurin hallaka wata karamar yarinya mai kimanin shekaru 4, da nufin yin balangu ko suya da namanta. Rahotanni sun bayyana cewa, yarinyar na wasa ne da sa'o'inta a kofar gida lokacin da Aliyu ya ja ta zuwa wani lungu yana kokarin yanka ta, yayin da wasu mutane suka gano shi. Kwamishinan 'yan sanda na jihar Legas Fatai Owoseni wanda ya tabbatar da labarin ya bayyana cewa, ana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin, yayin da aka mika wanda ake zargin ga ofishin' yan sanda na Denton dake yankin Oyingbo daga inda za a mika shi gaban kotu bisa zargin satar mutum da yunkurin kisan kai. Tuni dai aka mayar da yarinyar hannun mahaifiyar ta. Sai dai wani dan uwan wanda ake zargi mai suna Malam Isa, ya bayyana cewa dan uwan nasa ya dade yana fama da matsalar tabin hankali, ko da yake a baya an masa magani kamar ya warke sai yanzu kuma yake nuna alamun ciwon ya dawo masa. Isa ya ce, "ko a ranar da wannan al'amari ya faru suna kasuwa suna sayar da nama lokacin da ciwon ya tashi masa har ya barar da teburin naman ya fara yin wasu abubuwa na rashin hankali. Kafin mu farga ya cafko wannan yarinya da wukar yanka nama a hannun sa. Da kyar muka kama shi aka daure sannan aka nemo 'yan sanda. " Ko da yake wannan dan uwan Aliyu wanda ake zargi shi ma' yan sanda sun rike shi, amma ya yi korafin yadda shi da ya taimaka aka kai dan uwan nasa wajen hukuma, shi ma kuma ya an kama shi. ©Zuma Times Hausa

No comments:

Post a Comment

Pages