- Yayan kungiyar neman kafa kasar Biyafara, IPOB sun bazama farautar Hausawa - Matasan Inyamurai sun fara far ma Hausawa a garin Abia da Fatakwal Biyo bayan barkewar rikici tsakanin Sojojin Najeriya da yayan kungiyar rajin samar da kasar Biyafara, IPOB, garin Aba dake jihar Abia, yan kungiyar sun afka ma Hausawa. Wani bidiyo da yayi yawo a shafukan sadarwa na zamani ya nuna yadda matasan Iyamurai ke tsayar da motoci suna farautar Hausa-Fulani Musulmai, yayin da suka kona motoci da shagunan su. Majiyarmu ta ruwaito mutanen cikin motar suna yin magana da yaren Ibo, suna cewa su fa Inyamurai ne, kuma babu Hausawa a cikinsu, don haka su kyale su, su yi tafiyarsu.
Duk a cikin bidiyon an hangi matasan suna dauke da makamai, da suka hada da adduna, katakwaye da sauransu, haka zalika an hange abubuwa da dama akan hanya da suka kokkona, ciki har da motar Dangote. Zaku iya sauke wannnan bidiyon anan Download Here Ko kuma ku danna watch here domin kallon bidiyon a YouTube Watch Here
No comments:
Post a Comment