Sunday, September 3, 2017

(Tausayi) Yadda Ta Kashe Dan Kishiyarta Mai Kwanaki 14 Da Fiya-Fiya


Ta Kashe Dan Kishiyarta Mai Kwanaki 14 Da Fiya-Fiya *‘Yan Sanda Sun Kashe Mai Garkuwa Da Mutane A Bauchi *An Gano Wata Kungiya Mai Yanke Hukuncin Kisa A Bauchi Daga Khalid Idris Doya, Bauchi Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta hallaka wani mai garkuwa da mutane har lahira a tsaunin Dala dake karamar hukumar Dass a sa’ilin da suke fafatawa da wasu masu garkuwa da mutane a dajin. lamarin ya faru ne bayan da suka yi garkuwa da wata matar aure mai suna Na’ima Idris a kauyen Kundun. DSP Kamar Datti Abubakar jami’i mai magana da yawun rundunar a jihar ne ya shaida hakan a sa'ilin ganawarsa da manema labaru a Bauchi inda ya ke cewa sun yi nasarar kubutar da wata matar aure daga hanun masu garkuwa da mutane sai dai daya daga cikin masu garkuwar ya mutu a lokacin da suke fafatawa da jami’ansu na ‘yan sanda “A ranar 18/08/2017 wani mutum mai suna Aliyu Mohammed wanda kuma shi ne jami’i mai kula da asibitin bada magani na kauyen Kundun, Tafawa Balewa ya kawo rahoton wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da matarsa mai suna Na’ima Idris mai shekaru 25 inda suka bukaci ya basu zunzurutun kudi har naira miliyan goma (N10,000,000.00k)”. Datti ya kara da cewa “jami’anmu na sashin dakile aiyukan masu garkuwa da mutane sun samu nasarar ceto rayuwar ita Na’iman sai dai a lokacin da masu garkuwan suka ga ‘yan sanda sai suka bude musu wutu inda suma jami’anmu suka maida musu ruwan wuta a sakamakon hakan ne daya daga cikinsu ya mutu”. “A tsaunin Gala dake Dass ne masu garkuwan ke fakewa, inda muka yi nasarar kubutar da mutane Na’ima Idris, Yakubu Hussaini, da kuma wasu yara da suka yi garkuwa da su Inusa Alh. Usman mai shekaru 13 da Ishiaka Lawal mai shekaru 10. Abubuwan da muka kama a hanunsu sun bindiga 3, kakin soja, da bared da kuma abun dafa abinci”. Hakazakila, Rundunar ta ce wata mata mai suna Hindatu Abdullahi ta hallaka dan kishiyarta ta hanyar shayar da shi sinadarin fiya-fiya “A ranar 19/8/2017 jami’anmu sun samu rahoto a gidan wani mai suna Abudullahi Ori dake kauyen Wuro Bogga, Duguri a karamar hukumar Alkaleri, wanda a yanzu haka ya tafi aikin hajji ya kuma bar matansa su biyu a gida Fatima Abdullahi uwar gida, da Hindatu Abdullahi amarya. Ita amarya mai suna Hindatu ta shiga dakin uwar gida inda ta dauki danta mai suna Muhammad Abdullahi mai kwanaki 14 kacal a duniya inda ta bashi fiya-fiya a dakinta, a yayinda ya suma bayan da aka yi kokarin garzaya da shi asibiti yaron ya mutum”. In ji Datti A zantawarmu da ita Hindatu Abdullahi wacce ta amsa laifinta sai dai ta bayyana cewar tun usuli auren dole ne aka yi mata da shi wannan mutumin mai suna Abdullahi Ori “Akwai wanda na ke so, har an daura mana aure da shi a kotu babana ya ki amincewa duk gidanmu har ‘yan uwana kona na sona da shi, nima ina sonsa, Babana ne kadai baya sonsa ya dage aka aura min wannan alhajin, kuma gaskiya ina shan azaba sosai a gidansa, na rasa yanda zan yi tsautsayi ya kwasheni na aikata wannan mummunar aika-aikar”. In ji Hindatu Ta kara da cewa ita gaskiya ba tsananin kishi bane ya sanyata wannan aika-aikar illa dai kawai yanda uwar gidan ta rabata da mijin gabaki daya a yayin zamantakewar aurensu “Ni ina gidan ne kawai ina zaman gida, amma idan na je na fada wa babanmu halin da na ke ciki sai ya koreni ya dauki bulala ya dukeni ya ce karya na ke yi”. In ji wacce ta hallaka jaririn kishiyarta. Wakazalika, shalkwatanrundunar ‘yan sandan ta ce ta himmatu dakile aikace-aikacen wata kungiya mai kashe mutane da zarar suka yi wani laifin ba tare da jiran doka ta yi aiki a kansu ba DSP ya ce ‘Yan Sandan jihar sun himmatu dakile aniyar wata kungiya mai suna Ba-Beli wanda sukan hallaka mutum da zarar ya aikata dan wani laifi ba tare da jiran doka ta yi aiki a kansa ba, a bisa haka ne ma ya ce sun kama daya daga cikin mambobin wannan kungiyar mai suna Bello Abdullahi daga kauyen Basirka a jahar Jigawa “Shi wannan wanda muka kama da kansa ya amince cewar yana da hanu a kisan Ahmadu Musa Ardo dake kauyen Buzun, Ganjuwa, da kuma Musa Sale daga Balmo, Darazo”. A zantawarmu da wanda aka kama daga cikin mambobin ba-beli ya ce “sakamakon yawaitar masu garkuwa da mutane ne a yankin Dazaune ne wasu suka kafa kungiya inda suke kashe wasu ko su kai wasu kotu a lokacin da suka kamo su”. In ji shi DSP Kamal ya ce sun kuma yi nasarar kame wasu masu garkuwa da mutane, ‘yan fashi da makami, ‘yan sara suka da sauran laifukan ashsha a bangarori daban-daban na jihar Bauchi, inda ya ce suna ci gaba da gudanar da bincike a kansu da zarar suka kammala zasu gurfanar da su gaban kuliya. inda rundunar ta baje kolinsu wa manema labaru a makon jiya. Shalkwatan rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta bukaci jama’an jihar das u kasance masu kai rahoton dukkanin wani motsin da basu amince das hi ba zuwa ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa, ko kuma su kira shalkwatan kai tsaye ta wannan lambar don kai rahoton gaggawa ko neman dauki lambar ita ce 08151849417.

src Rariya

No comments:

Post a Comment

Pages