Hukumar NSCDC ta cafke wasu masu satar mutane a Kwantagora Hukumar NSCDC ta cafke mutum uku masu satar mutane a Kwantagora - Mutanen sun amsa laifin su da zuwa kwantagora don su kware a sana'arsu ne - Matar da aka sace a watan baya a garin ta shaida su suka sace ta Hukumar NSCDC sashen jihar Niger ta fidda rahoton cafke wasu mutane uku da ake zargi da sace-sacen mutane a garin Kwantagora. Mista Philip kwamanda a hukumar na jihar ya bayyana hakan ne a ganawar da aka yi da shi a ranar Alhamis da NAN.
Ya ce an kama mutanen ne a gidan da suke buya a garin Kontagora bayan zagayen binciko su da aka yi. Ya kara da cewa mutanen dama sun addabi ‘yan unguwar tasu da sace-sace a kwanakin baya. Mista Ayuba ya kara da cewa 'mutanen sun ansa laifin su da cewar zuwan su Kontagora domin su kware ne don akwai wasu shahararrun mutane da suke so su sace a garin.'
Shugaban ‘yan kungiyar da aka kama an kama shi sanye da kayan soja, tare da bel da takalman soja, rigunan kaki da bindigar wasa da mota. Wata mata da aka sace a garin watan da ya wuce ta shaida daya daga cikin barayin da motar da suka sa ta a ciki da suka sace ta.
No comments:
Post a Comment