Makarantar horas da soji da ke Kaduna ta fitar da sunayen daliban da sukayi nasarar shiga
An fitar da sunayen daga kowace Jiha a fadin kasan nan - 'Yan wucin gadi zasu dakata har sai idan an gayyace su - NDA tana gudanar da PGD da Msc da Ph.D ga farar hula A ranar laraba ne makarantar horas da sojoji na kasa wato NDA ta fitar da sunayen wadanda suka samu nasarar tsalleke gwaji da aka gudanar daga 8 na Yuli zuwa 26 na Agusta 2017. An fitar da sunayen ne daga ko wace jiha a fadin kasan nan. Har wayau, an fitar da sunayen 'yan wucin gadi amma dai za su dakata sai idan akwai bukatan a gayyace su. NDA ita ce kadai jami'a na horas da sojoji a Najeriya. Shekaru hudu dalibai suke yi don kammala digiri na farko, shekaru 4 na karatun cikin aji sai kuma shekara daya na horon soja. An kafa NDA ne a shekarar 1964 wanda take da alhakin horas da sojojin kasa da na ruwa da na iska. Da kafuwar ta, ta fara da dalibai 62 wanda yawancin su kananan sojojin kasa ne. Daga baya ta habaka zuwa horas da dukkan nau'in soja a shekarar 1978. A shekarar 1985 makarantar ta fara gudanar da karatun digiri na farko ga sojojin da suke kan aiki. A yanzun kuwa har tana gudanar da karatun sharan fage don digiri na biyu (PGD) da digiri na biyu (Msc) da kuma digiri na uku (Ph.D) ga sojoji da farar hula. Ga sunayen wadanda sukayi nasarar a kasa.
No comments:
Post a Comment