Friday, September 1, 2017

Farashin man fetur zai sauka nan ba da dadewa ba - Kachiku


Farashin man fetur zai sauka nan ba da dadewa ba - Kachiku Farashin man fetur zai sauko nan da watanni hudu zuwa biyar - Tun shekaru 10 da suka wuce, yanzu ne kawai matatun mai guda 3 ke aiki gaba daya -Karamin ministan yace gwamnati zata canza bututun mai da suka shekara 35 suna aiki A jiya ne Dr. Ibe Kachikwu, karamin minista na ma'adanan man fetur yayi hasashen cewa man fetur mai saukin farashi na nan tafe. Yayi wannan hasashen ne ganin yadda farashin man disel ya sauka sakamakon yawaita da yayi a kasuwan mai. A cewar sa, farashin sauran ma'adanai na man fetur zasu sauka nan da wata 4 zuwa 6, Hasali ma wannan ne karo na farko cikin shekaru 10 da matatan man fetur duka guda ukun suke aiki a lokaci daya duk da dai ba dari bisa dari ba. Da sannu zamu mayar da su cikin su aiki dari bisa dari'' in ji shi. Ya kara da cewa ''wannan ne karo na farko da aka bunkasa ma'ajiyan man fetur guda 16 cikin 19 da ake da su''. Ya kuma ce gwamanati tana da kudirin yin wadansu gyaran. A nasa ra'ayin, lokaci yayi da zamu magance duk wani matsala. Yin hakan shi zai ba kamfanoni daman sayar da mai a farashin da ya dace. Za'a samar da ayyukan yi kimanin 200,000. Idan kuwa mun ci gaba a tafarkin da muke kai a da ayyukan mutane kimanin 400,000 zasu salwanta.

Ya ce sun gaji bashi wanda faga bisani suka biya ta naira biliyan 600 daga tsohuwar gwamnati da 'yan kasuwan mai suke bi sakamakon hakan ya sa 'yan kasuwan suka daina shigo da mai . Wannan shi ya janyo karancin mai tare da kasancewan tsarin tallafin man fetur baya tasiri sai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gwammace ya tafiyar da kudin tallafin ta ciyar da kasa gaba. Don haka sai aka cire tallafin. kasancewar an katange 'yan kasuwan daga amfanuwa da romon tallafi ya janyo tashin farshin mai ga al'umma. Ya kara da cewa a lokacin kasar bata da wani matatan mai da yake aiki ballantana a samu saukin farshi. Dole ya sa aka bar 'yan kasuwa su shigo da mai su sayar a farashin da zasu samu mafita wanda farashi ne mai tsada. Yanzun dai al'amurra sun fara daidaita tunda ga shi ana tace gangan mai guda 445 a kullum a matatan mu na gida Najeriya.

No comments:

Post a Comment

Pages