Farare Da Ƙyawawan Mata Yanzu Ake Sawa A Film - Maryam Sangandale
Farare Da Ƙyawawan Mata Yanzu Ake Sawa A Film - Maryam Santander. Daga : Sharifuddeen Baba, Kano. Maryam A Baba wacce akafi sani da Maryam Sangandali na ɗaya daga cikin mawaƙan Hausa na zamani da tauraruwarsu ke haskawa a wannan ƙarnin, itama ta halarci taron marubuta na duniya da aka gudanar cikin makon da ya gabata, Kannywoodtoday ta samu zarafin tattaunawa da ita inda ta warware zare da abawar salon waƙoƙiinta. Sangandale tace ta zaɓi salon waƙa cikin ruwan sanyi ne wanda tace hakan ya fi gamsar da masu sauraro tare da nishaɗantar da masu sauraro. Da aka tambayeta ko me ne dalilin da ako da yaushe akafi ganinta da Aminu Alan waqa, sai ta amsa da cewar "ko shakka babu fahimta ce tazo ɗaya dashi, musamman idan aka dubi shima irin salon rera waƙarsa kenan, kuma yana taimakamin wajen gyaramin waƙoƙina tare da yimin gyara, wani lokaci ma ya rubuta min yace ga yadda waƙar zata kasance. Wannan tasa ake ganin muna Kamanceceniya cikin waƙoƙinmu". Sannan Maryam A Baba ( Mayam Sangandale) ta bayyawa Kannywood today cewar tun ina firamare nake sha’awar waƙoƙi, saboda haka na ƙudurce a zuciyata cewar idan na gama makaranta nima zan bayar da tawa gudunmawar. Haka kuma an tamabayi Maryam Sangandali shin me yasa bata fita a fina-finan Hausa? Sai ta ce "gaskiya iyaka cina waƙa kawai, kasan su fim ana ɗaukar kyawawan mata kuma farare ne, to mu da muke haka sai mu tsaya iya waƙar kawai. Aƙarshe Maryam Sangandali ta bayyana gamsuwarta da wannan taro.
Hausamini
No comments:
Post a Comment