Friday, September 8, 2017

2019: Abunda zai faru da yan Najeriya idan Buhari ya yanke shawarar sake tsayawa takara – Shehu Sani ya bayyana


Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa hukuncin Buhari na tsayawa takara ko kin tsayawa takara a 2019, zai zamo illa ga yan Najeriya da dama - Sanatan ya bayyana cewa duk irin hukunci da ya yanke, zai shafi gwamnatin kasar da makomar wasu mutane - Sani ya bayyana cewa shugaban kasar na bin wasu dabaru da shawarar da zai dauka, sannan ya maida hankali wajen cika alkawaran da ya dauka ma yan Najeriya a wannan lokaci Sanata dake wakiltar yankin Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa duk abunda shugaban kasa Muhammadu Buhari yace game da kudirinsa na tsayawa takara karo na biyu zai samu sakamakonsa a kan yan Najeriy da dama. Dan majalisar ya bayyana cewa yayinda shugaba Buhari yaki cewa komai kan kudirinsa a zaben 2019, babu mamaki yana kokarin ganin ya maida hankali wajen cika alkawaran zaben da ya dauka. Ya bayyana hakan a jiya a lokacin da ya fito a wani shirin talbijin din Channels TV mai taken ‘Siyasa a Yau’ wato ‘Politics Today’ wanda Seun Okinbaloye ya gabatar. “Babu wanda zai iya fadin ko shugaba Buhari zai tsaya takara a 2019. Amma a bayyane yake cewa idan ya yanke shawarar cewa ba zai tsaya takara ba hakan na nufin karshen gwamnati a Najeriya saboda zai kasance iya 2019 ne sannan ida yace zai zai tsaya takara, babu shakka siyasar mutane da dama zai zo karshe.

Amma ina ganin yana bin wasu dabaru ne a yanzu, yana so ya cika alkawaran da ya dauka a 2015 sannan kuma duk abunda ya fito daga bakin sa yana da matukar tasiri ga gwamnatin Najeriya kamar yadda yake a yanzu.”

No comments:

Post a Comment

Pages