Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya kashe zama da Ministocin sa na yau
Shugaban kasa Buhari ya soke taron Majalisar 'FEC' na makon yau - Majalisar zartarwa ba za ta zauna ba yau Inji Fadar Shugaban kasa - Shugaba Buhari zai karbi wani rahoto daga Mataimakin Shugaban kasar Labari ya zo mana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kashe zama da Ministocin sa na wannan makon.
Fadar Shugaban kasa tace Shugaba Buhari ya soke taron Majalisar zartarwa na Tarayya watau 'FEC' da ya kamata ayi yau. Majalisar ba za ta zauna ba Inji mai magana da bakin Shugaban kasar watau Femi Adesina.

Adesina ya bada dalilin da ya sa ba za ayi taron ba. Yace Shugaban kasa Buhari zai karbi wani rahoto na musamman ne gane da tsohon Sakataren Gwamnatin kasar Babachir Lawal sa Shugaban NIA da aka dakatar kwanaki daga Mataimakin Shugaban kasar Yemi Osinbajo. A jiya dai Mun ji cewa an nemi Shugaban kasa Buhari ya bayyanawa 'Yan Najeriya halin rashin lafiyar sa kowa ya san abin da ake ciki.
No comments:
Post a Comment