Hindatu ta bayyana ma manema labarai a hedkwatan 'yan sanda na Jihar bauchi yadda ta auri mijinta a matsayin matarsa ta biyu ba a son ranta ba sai don bin umurnin iyayenta. Ta bayyana yadda suke zaman doya da manja tsakaninta da mijin ta da kishiyarta. Daga bisani dai mijin nata yana son ta amma kwatsam sai ya fara gallaza mata yana cutar da ita. Iyayenta basu yarda da maganarta ba ko da ta kai masu koke, a cewar ta.
Hindatu dai ta tabka wannan danyen aiki ne Alhali mijin nata yana saudiyya don aikin hajji ita kuna kishiyar nata bata gida. A cewar ta, ta dauki jinjirin kishiyar nata dan wata biyu ta kai shi dakinta a inda tayi kokarin sharyar da shi guban sai ya ki sha. Nan take ta yi farga da munin aikin da tayi niyya tayi maza ta cire rigar sa ta share masa gubar da rigar.Hindatu dai tayi ikirarin yin nadama a duk lokacin da ta tuna da wannan danyen aiki. Ta kuma ce a shirye take da fuskanci duk wani hukunci da za'a zartar a kanta. Ta kuma kara da cewan Mijin nata da aka kira shi ta waya yayi alwashin sakin ta da zaran ya dawo daga aikin hajji.
-naij
No comments:
Post a Comment