Wednesday, August 23, 2017

Yadda Dubun wani makahon karya tacika a legas

-Abdullahi Abbas haifaffen jihar Oyo ne -Kudin da yake samu yafi albashin masu gadin unguwan -Bincike ya nuna cewa yana cikin kungiyan nakasassun mabaratan karya dake yaudaran mutane NAIJ.com ta samu rahoton wani makahon karya mai suna Abdullah Abbas da aka kama a unguwan Ikorodu dake jihar Legas a lokacin da yake bara. Kafin akama shi a ranar 21 ga watan Agusta, Mutane sun ce sun saba ganin Abdullahi Abbas a akan titin Ikorodu tare da wani karamin yaro dan shekara 12 yana mishi jagora. Bayan an kama shi, Abbas ya bayyana cewa yana samun N5500 zuwa N8000 a kowani rana daga bara. Sama da albashin mutane dayawa a First da Odogunyan.

A rahoton da NAIJ ta samu, An kama Abbas ne bayan yagama ganawa da wani mazaunin unguwan mai suna Adeoye Baliks, a lokacin da suke ganawan ne ya gano Abbas makaho bane sai ya tona ma sa asiri a take a wajen.

A lokacin da aka mishi bincike, an gano cewa haifaffen jihar Oyo ne kuma yana daga cikin wata kungiyan nakasassun mabarata da ke yaudarar mutane a jihar. Abbas ya samu nasarar fita da ran sa daga hannun fusattatu mutane a lokacin da yansandar suka isa wajen.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausazone

No comments:

Post a Comment

Pages