Sarakunan gargajiya a jihar Katsina sun yi lale maraba da Buhari a Daura (Hotuna)
Shugaba Muhammadu Buhari ya sadu da sarkin Daura da tawagarsa yayin da ya isa Daura - Gwamnan jihar Katsina na cikin shuganin da suka yi maraba da shugaba Buhari a Daura - Manjo Janar Adeniyi Oyebade na GOC 1 Division Nigerian Army ya kasance daya daga cikin wadanda suka tarbi shugaba Buhari a Daura A safiyar ranar Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar birnin tarayya Abuja zuwa garinsa Daura domin yin hutun sallah, bayan da shugaban ya sauka, shugabanin da dama wadanda ke jiran izowar shugaba Buhari a Daura sun hada gwamnan jihar Katsina da sarakunan gargajiya da jami’an tsaro da manyan ‘yan siyasa. Kamar yadda Majiyarmu ke da labari, shugaban kasa Muhamadu Buhari ya sadu da sarkin Daura mai martaba Alhaji Umar Faruk Umar tare da tawagarsa yayin da ya isa Daura a jihar Katsina a gaban bikin Eid El Kabir da za a yi a ranar 30 ga watan Agusta, 2017.
Daga bisani shugaba Buhari ya kuma gaisa da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari da mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman da kuma kwamandan sojoji na GOC 1 Division Nigerian Army, Manjo Janar Adeniyi Oyebade a lokacin da ya isa Katsina.
No comments:
Post a Comment