NAIJ ta tattaro cewa jami'iyyar zata tsaida dan Arewa ne a matsayin dan takarar shugaban kasa sannan shugabancin jami'iyyar zata koma sashin kudu. Kishin-kishin: Dangote ne dan takarar a PDP 2019 Wata majiya a jami'iyyar PDP tace ziyarar da jami'iyyar aka kai ma Alhaji Aliko dangote bazai rasa nasaba ta yi masa tayin tsaya wa takarar shugabancin kasa a karkashin tutar jami'iyyar. Majiyar tace tuni an ma riga an aike tawagar da zata je zawarcin Aliko Danote, an yanke shawaran hakan ne bayan kwamitin jami'iyyar wanda ta hada da tsohon shugaba Goodluck Jonathan sun tattauna kuma suka yarda cewa shine ya dace yayi musu takara.
"Ina tabbatar maka da cewa jami'iyyar PDP tana zawarcin Alhaji Aliko Dangote domin ya zo yayi takarar shugabancin kasa a karkashin tutar jami'iyyar a zaben shekara 2019.'' "Anyi la'akari da abubuwa masu yawa kafin shawarar a neme shi. Alhaji Dangote mutum ne mai mutunci da kima a idon jama'a, kuma yayi suna a duk fadin duniya kuma har ila yau yana da kudin da zai iya daukan nauyin duk wani abu da ka iya tasowa wajen fafutukar yakin neman zabe. Mun tabbata zai iya tunkarar duk wani wanda jami'iyyar APC zata tsayar," a cewar majiyan. Hakazalika, bincike da jaridar Daily Times tayi ya nuna cewa attajirin ya bada gudunmawa wajen yakin neman zaben wasu shugabanin kasar Najeriya. Wani mamba na kwamitin rikon kwarya na Ahmed Makarfi yace sai nan gaba zasuyi tsokaci akan maganar.Daga karshe, wani na hannun daman Aliko Dangote da ya nemi a sakaya sunan sa yace Dangote bashi da ra'ayin takarar siyasa, shi yafi son ya cigaba da saka hannun jari a kamfanoni da kuma samar wa da jama'a aikin yi.
No comments:
Post a Comment