Illar da cinnikin bayi ya yiwa nahiyar Afrika
An fara wani taron kasa da kasa na kwanaki uku domin duba irin illar da cinniki bayi ya yiwa nahiyar Afrika
Laraba aka fara wani taron kasa da kasa na kwanaki uku domin jawo hankalin bakakken fata dake zaune a kasashen turai da Amurka, su dawo Afrika domin zama ko kuma zuba jari a wani farni.
Bikin ko kuma taron ya kuma dubbi irin illar da cinnikin bayi ya yiwa Nahiyar Afrika.
‘Yan asalin Afrika daga sassa dabam dabam na duniya suke halarta wannan taro da aka shirya domin tunawa da cinnikin bayi da aka gudanar a duniya fiye da shekaru 300 da suka shige.
Mr Bobbi, daya daga cikin bakaken fata da suka yi kaura daga kasar Amurka, suka koma Afrika wanda kuma yake zaune a kasar Ghana a halin yanzu, ya baiyanawa wakilin sashen Hausa Babangida Jibirin dalilinsa na yin wannan kaura.
Yace ya kaura ne domin yafi ganewa zaman Afrika a matsayin wanda aka bautar da kakanisa shekaru aru aru. Yace yana ganin a Afrika ne zai sake ya kuma wala.
Bikin na bana na zuwa ne a daidai lokacinda kasashen Afrika suka tashi tsaye wajen hana yan nahiyar tsalakawa zuwa kasashen turai da Amurka.
Mrs Abike Dabri, wadda take baiwa shugaban Nigeria shawara akan harkokin ‘yan kasashen waje. Tace shawarta ga wadanda ke kokarin zuwa kasashen turai da Amurka su daina tsalakawa zuwa turai suna kashe kan su, a yayinda wasu daga kasashen turai da Amurka ke dawowa.
Wata mace mai suna Malama Amina ‘yar asalin garin Badagry dake Lagos ta fadawa wakilin sashen Hausa Babangida Jibirin yadda take ji gameda taron da ake gudanarwa na tunawa da cinnikin bayi.
-Voahausa
No comments:
Post a Comment