Shugabannin Nijeriya Da Sauran Mahajjatan Nijeriya Sun Gabatar Da Addu'oi Na Musamman Ga Kasa A Filin Arfa
A yammacin yau Alhamis kuma ranar Arfa tawagar Malaman Naijeriya ta gudanar da addu'oi na musamman ga ƙasar Naijeriya, ƙarƙashin jagorancin Amirul Hajji na ƙasa na bana, Mai martaba Sarkin Bauchi, (Dr. Rilwanu Suleiman Adamu).
Shugaban Izalar Naijeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, Sheikh Tijjani Bala Ƙalarawiy sheikh Yaƙubu Musa Hassan na ɗaya daga cikin waɗanda suka gabatar da addu'on, Malaman sun roƙi Allah zaman Lafiya mai ɗorewa ga ƙasar Naijeriya, tare da roƙawa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari lafiya da zama lafiya, da kuma sauran buƙatun ƙasa da ƴan ƙasa. Gwamnan Jihar Borno Ƙashim Shettima, Gwamnan Bauchi Muhammad Abubakar, da Gwamnan Jigawa Badaru Talamiz, Ministan jiragen sama Hadi sirika da tsohon ministan Abuja Dr. Aliyu Modibbo Umar tare da manyan ƴan majalisar Dattawa irin su Sanata Ahmad Sani yerima, sanata Ndume dana Dokoki na tarayya, da zunzurutun Jama'a mahalarta Tsayuwar Arfa ne suka halarci gabatar da Addu'oin.
No comments:
Post a Comment