Wani wanda su ka dade da Shugaba Buhari yace dole ya rabu da Mamman Daura - Lawal Idris wanda yace su suka jawo Buhari siyasa amma yanzu kuraye sun zagaye sa - Wannan mutumi yace Mamman Daura ne babbar matsalar Shugaban kasa Buhari Kwanaki Lawal Idris Wani wanda su ka dade da Shugaba Buhari tun shekaru 45 da su ka wuce yace dole Buhari ya rabu da Mamman Daura don kuwa shi ne babban matsalar sa.
Malam Idris yace tun lokacin da zai janyo Muhammadu Buhari siyasa aka fada masa cewa dole ya bi a hankali da Mamman Daura. A hirar sa da Jaridar Daily Trust yace Mamman Daura ba ya goyon bayan Buhari ya zama Shugaban kasar.
Lawal Idris ya bayyana cewa mafi yawan Ma'aikatan da ke tare da Shugaban kasar irin su Abba Kyari duk Mamman Daura ne ya kawo su. Yake cewa Abba Kyari yaron Mamman Daura ne don haka aka kyale sa yake cin karen sa babu babbaka. Aminin Shugaban kasar yace dole Buhari ya guji Mamman Daura idan har ana so abubuwa su dawo daidai kamar yadda yake sa rai.
©Naij
No comments:
Post a Comment