Jamila Umar Turaki, wadda aka fi sani da 'Jamila Nagudu' ba boyayya ba ce ga duk mai kallon fina-finan Hausa. Ta dade ana damawa da ita a industirin fina-finan Hausa. A watan da ya gabata ne jarumar sanya a hannun zama jakadiyar maggi Vedan a lagos.
A jiya ne jarumar ta sanya wani Hoto a shafin ta na Instagram, hoton wanda ke nuni da cewa tana gadon asibiti inda ta turo shi a shafin na ta ta rubuta 'Sick' ma'ana rashin lafiya. Tura hoton ke da wuya dimbin masoyan ta su ka ci gaba da yi mata addu'ar samun sauki.
A gefe guda kuma wasu suna tambayar: Me ke damun Jarumar? Mun yi kokarin kiran jarumar domin mu jajanta mata tare da tambayar ta halin da ta ke ciki amma abin ya ci tura don kuwa duka lambobin wayar ta a kashe suke.
Sai dai mun samu tattaunawa da Manajan Jarumar mai Suna Usman Usee, wanda ake kira da 'Usee Light' Inda ya tabbatar mana da cewa jarumar ta na jin sauki sannan idan anjima da karfe na ranar za a yi jarumar Tiyata (Operation) Sakamakon cutar Appendix (Cutar Tsakuwar Ciki) da ke damun ta. Yanzu haka dai a yau Alhamis, 13 ga watan yuli 2017. Za a yi wa jarumar Tiyata a wani Asibitin kudi mai suna "Garden City' da ke garin kaduna.
Muna fatan Allah ya bata Lafiya.
©Kannywood
No comments:
Post a Comment