Monday, July 24, 2017

Jaruma rahama sadau ta yiwa BBC karya a hirar da sukayi

Jarumar ta bayyana hakan ne a wata hira da tayi da BBC Hausa a babban birnin tarayya Abuja. A cewar Rahama itama gani tayi kamar yadda kowa ya gani a kafafen yada labarai cewar an kore ta amma dai ita babu wanda ya aika mata rubutacciyar wasika a kan haka.
Rahma ta bayyana kamar haka

Ni fa babu wanda ya kore ni daga Kannywood. Har izuwa yanzu da nake Magana ba wani wanda ya aiko mani da rubutaciyyar wasika dake nuni ga sallama ta daga kamfanin.
“An rage gani na a shirin fina-finai ne saboda, kamar yadda na gaya maka, ina fitowa a fina-finan kudu wato Nollywood da kuma gudanar da sauran al’amura da suka danganci rayuwa ta.
Amma yanzu zan koma yin fim na Hausa gadan-gadan musamman ganin irin nasarar da na samu a fim dina na Rariya. Zan ci gaba da daukar nauyin fim baya ga fitowa a ciki da zan ci gaba da yi.

Sai dai kuma sakataren kungiyar dake ladabtar da ýan wasa wato MOPPAN, Salisu Mohammed ya karyata maganar Rahama. Baya ga haka ya bayyana cewa ta ce baá aika mata rubutaciyyar wasika bane kan korar tata saboda tana neman suna.
-Kannywood

No comments:

Post a Comment

Pages