Thursday, July 20, 2017

Hotunan yadda direbobi suka yi kaca-kaca da bankuna a Lagos

Kallli hotunan yadda direbobi suka kona wasu bankuna a Legas bayan sun fusata sakamakon kashe daya daga cikinsu da ake zargin 'yan sanda sun yi.
Bayan sun kashe direban, sai 'yan sandan suka shige cikin bankin Diamond domin neman mafaka lamarin da ya sa direbobin suka cinna wa bankin da bankin Sterling me makwabtaka wuta.
Wani bangare na bankunan da aka kona a anguwar Apapa da ke Legas, yankin da aka sani da yawan hada-hadar jama'a da ababen hawa.
Rahotanni sun ce direbonin manyan mota ne suka kona bankunan bayan an kashe daya daga cikinsu, kuma ba bata lokaci aka tura 'yan sandan kwantar da tarzoma.
Wutar da direbobin suka cinna ya kama bankin Diamond ne da bankin Sterling, sai dai zuwa yanzu ba a san irin yawan barnar da aka yi wa bankunan ba.
A Najeriya dai an dade ana zargin 'yan sanda da harbe mutane ba bisa ka'ida ba kuma ana zargin mutane da daukar doka a hannayensu.-bbchausa

No comments:

Post a Comment

Pages