Tuesday, August 15, 2017

LABARI DA DUMIDUMINSA An Yi Wa Charly Boy Jina-jina A Abuja


LABARI DA DUMIDUMINSA An Yi Wa Charly Boy Jina-jina A Abuja Daga Aliyu Ahmad. Rahotanni sun nuna cewa mafusata sun tarwatsa jagoran zanga-zangar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki, wato Charly Boy da shi da tawagarsa sun shiga hannun mafusata a yayin da suke tattakin zanga-zangar Buhari ya sauka daga mulki. Lamarin ya auku ne a daidai lokacin da Charly Boy da tawagarsa suke kokarin shiga kasuwar Wuse dake Abuja, amma masu tsaron kasuwar suka hana shiga. Daga bisani da Charly Boy sun yi yunkurin shiga kasuwa da karfi da yaji, inda har wasu daga cikin su sun shiga, sai mafusata wadanda akasarin su Hausawa ne suka farma tawagar nasa inda suka raunata wasu daga cikin su tare da farfasa musu motoci. Yanzu haka dai jami'an tsaro sun rufe kasuwar ta Wuse don gudun abinda ka iya biyo baya. -Rariya

No comments:

Post a Comment

Pages